English
A A A A A

Mattiyu 13:31-58
31. Ya ba su wani misali ya ce: “Mulkin sama yana kama da ƙwayar mustad, wadda mutum ya ɗauka ya shuka a gonarsa.
32. Ko da yake ita ce mafi ƙanƙanta cikin ƙwayoyinku, duk da haka saʼad da ta yi girma, takan zama mafi girma cikin tsire-tsiren lambu ta kuma zama itace, har tsuntsayen sararin sama su zo su yi sheƙa a rassansa.”
33. Har yanzu ya ba su wani misali ya ce: “Mulkin sama yana kama da yisti wanda mace ta ɗauka ta kwaɓa garin alkama mai yawa, har sai da yistin ya garwaye yistin duka.”
34. Yesu ya faɗa wa taron dukan waɗannan abubuwa cikin misalai; bai faɗa musu kome ba, sai tare da yin amfani da misalai.
35. Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta wurin annabi cewa: “Zan buɗe bakina da misalai, zan faɗi abubuwan da suke ɓoye tun halittar duniya.”
36. Saʼan nan ya bar taron ya shiga gida. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa suka ce, “Bayyana mana misalin ciyayin nan a gona.”
37. Ya amsa ya ce, “Mai yafa irin mai kyan nan, shi ne Ɗan Mutum.
38. Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ʼyaʼyan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ʼyaʼyan mugun nan,
39. abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne malaʼiku.
40. “Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani.
41. Ɗan Mutum zai aiki malaʼikunsa, su kuwa cire daga mulkinsa kome da yake jawo zunubi da kuma duk masu aikata mugunta.
42. Za su jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.
43. Saʼan nan masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yǎ ji.”
44. “Mulkin sama yana kama da dukiyar da aka ɓoye a gona. Da wani ya same ta, sai yǎ sāke ɓoye ta, saʼan nan cikin farin cikinsa yǎ je yǎ sayar da duk abin da yake da shi yǎ sayi gonar.
45. “Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman luʼuluʼai masu kyau.
46. Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi.
47. “Har yanzu, mulkin sama yana kama da tarun da aka jefa cikin tafki yǎ kamo kifi iri-iri.
48. Da tarun ya cika, masuntan suka jawo shi gaci. Sai suka zauna suka tattara kifi masu kyau a kwanduna, amma suka zubar da marasa kyau.
49. Haka zai kasance a ƙarshen zamani. Malaʼiku za su zo su ware masu mugunta daga masu adalci
50. su kuma jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”
51. Yesu ya tambaye, su ya ce, “Kun gane dukan waɗannan abubuwa?” Suka amsa, “I.”
52. Saʼan nan ya ce musu, “Saboda haka duk malamin dokokin da ya horu game da koyarwar mulkin sama, yana kama da maigida wanda yakan fitar daga ɗakin ajiyarsa sababbin dukiya da kuma tsofaffi.”
53. Saʼad da Yesu ya gama ba da waɗannan misalai, sai ya ci gaba daga can.
54. Yana isowa garinsa, sai ya fara koya wa mutane a cikin majamiʼarsu, suka kuwa yi mamaki. Suka yi ta tambaya suna cewa, “Ina wannan mutum ya sami irin wannan hikima da kuma ayyukan banmamaki haka?
55. Wannan ba shi ne ɗan kafinta nan ba? Ba mahaifiyarsa ba ce Maryamu, ʼyanʼuwansa kuma Yaƙub, Yusuf, Siman da Yahuda ba?
56. Duk ʼyanʼuwansa mata kuma ba tare da mu suke ba? To, a ina wannan mutum ya sami dukan waɗannan abubuwa?”
57. Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.”
58. Bai kuwa yi abubuwan banmamaki da yawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.