English
A A A A A

Mattiyu 13:1-30
1. A ranan nan sai Yesu ya fita daga gida ya je ya zauna a bakin tafkin.
2. Taron mutane mai yawan gaske suka taru kewaye da shi har ya kai sai da ya shiga jirgin ruwa ya zauna, yayinda dukan mutane suka tsaya a gaci.
3. Saʼan nan ya faɗa musu abubuwa da yawa cikin misalai, yana cewa: “Wani manomi ya fita don yǎ shuka irinsa.
4. Da yana yafa irin, waɗansu suka faffāɗi a kan hanya, tsuntsaye kuwa suka zo suka cinye su.
5. Waɗansu suka faffāɗi a wurare mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira, da yake ƙasar ba zurfi.
6. Sai dai da rana ta ɗaga, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka kuma yanƙwane domin ba su da saiwa sosai.
7. Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya, ƙayan kuwa ta yi girma ta shaƙe su.
8. Har wa yau, waɗansu irin suka faffāɗi a ƙasa mai kyau, inda suka ba da amfani-riɓi ɗari, sittin ko kuma talatin na abin da aka shuka.
9. Duk mai kunnen ji, yǎ ji.”
10. Almajiran suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Me ya sa kake wa mutane magana da misalai?”
11. Ya amsa ya ce, “Sanin asirin mulkin sama kam, ku aka ba wa, amma ba su ba.
12. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, zai kuwa samu a yalwace. Duk wanda kuma ba shi da shi, ko ɗan abin da yake da shi ma, za a karɓe.
13. Abin da ya sa nake musu magana da misalai ke nan: “ ‘Ko da yake suna ƙallo, ba sa gani; ko da yake suna saurara, ba sa ji ko su gane.’
14. A kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa: “ ‘Za ku yi ta ji amma ba za ku taɓa ganewa ba; za ku yi ta ƙallo amma ba za ku taɓa gani ba.
15. Gama zuciyar mutanen nan ta taurare; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. Da ba haka ba, mai yiwuwa su gani da idanunsu, su kuma ji da kunnuwansu, su gane a zuciyarsu, su kuwa juya, in kuma warkar da su.’
16. Amma idanunku masu albarka ne domin suna gani, haka ma kunnuwanku domin suna ji.
17. Gama gaskiya nake gaya muku, annabawa da mutane masu adalci da yawa sun yi marmarin ganin abin da kuke gani amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji amma ba su ji ba.
18. “To, ku saurari maʼanar misali na mai shukan nan.
19. Duk saʼad da wani ya ji saƙo game da mulkin bai kuwa fahimce shi ba, mugun nan yakan zo yǎ ƙwace abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya fāɗi a kan hanya.
20. Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a wuraren duwatsu kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, nan da nan kuwa yǎ karɓe ta da murna.
21. Sai dai da yake ba shi da saiwa, yakan ɗan jima kaɗan kawai. Da wata wahala ko tsanani ya auko masa saboda maganar, nan da nan sai yǎ ja da baya.
22. Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi cikin ƙaya kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, sai dai damuwoyin rayuwan nan da jarabar arzikin duniya sukan shaƙe shi, yǎ sa maganar ta kāsa amfani.
23. Amma wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a ƙasa mai kyau, shi ne mutumin da yakan ji maganar yǎ kuwa fahimce ta. Yakan ba da amfani wani riɓi ɗari, sittin, ko talatin na abin da aka shuka.”
24. Yesu ya ba su wani misali: “Mulkin sama yana kama da wani da ya shuka iri mai kyau a cikin gonarsa.
25. Amma yayinda kowa yake barci, abokin gābansa ya zo ya yafa ciyayi a cikin alkamar, ya tafi abinsa.
26. Saʼad da alkamar ta tashi ta yi kawuna, sai ciyayin ma suka bayyana.
27. “Bayin mai gonar suka zo wurinsa suka ce, ‘Ranka yǎ daɗe, ashe, ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? To, ina ciyayin nan suka fito?’
28. “Sai ya ce, ‘Abokin gāba ne ya yi wannan.’ “Bayin suka tambaye shi suka ce, ‘Kana so mu je mu tuttumɓuke su?’
29. “Ya amsa ya ce, ‘Aʼa, don kada garin tuttumɓuke ciyayi, ku cire har da alkamar.
30. Ku ƙyale su su yi girma tare sai lokacin girbi. A lokacin zan gaya wa masu girbi: Da fari ku tara ciyayin ku kuma ɗaure su dami-dami don a ƙone; saʼan nan ku tara alkamar ku kuma kawo su cikin rumbuna.’ ”