A A A A A

Mattiyu 12:1-21
1. A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci.
2. Saʼad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.”
3. Sai ya amsa, ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne saʼad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa?
4. Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin-wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai.
5. Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba?
6. Ina faɗa muku cewa wani wanda ya fi haikali yana a nan.
7. Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’ da ba ku zargi marar laifi ba.
8. Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”
9. Da ya ci gaba daga wurin, sai ya shiga majamiʼarsu,
10. a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?”
11. Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba?
12. Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a yi alheri ran Asabbaci.”
13. Saʼan nan ya ce wa mutumin, “Miƙa hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan.
14. Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu.
15. Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu,
16. yana jan musu kunne kada su faɗa wa kowa akan ko shi wane ne.
17. Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya ne cewa:
18. “Ga bawana da na zaɓa, ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi; zan sa Ruhuna a kansa, zai kuma yi shelar adalci ga alʼummai.
19. Ba zai yi faɗa ko yǎ ɗaga murya ba, ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna.
20. Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba. fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara.
21. Cikin sunansa alʼummai za su dogara.”