A A A A A

Mattiyu 10:21-42
21. “Ɗanʼuwa zai ci amanar ɗanʼuwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ʼyaʼya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.
22. Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.
23. Saʼad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Israʼila, Ɗan Mutum zai zo.
24. “Ɗalibi ba ya fin malaminsa, haka ma, bawa ba ya fin maigidansa.
25. Ya isa wa ɗalibi yǎ zama kamar malaminsa, haka ma bawa kamar maigidansa. In har an kira wanda yake kan gida, Beʼelzebub, me za su ce game da mutanen gidansa?
26. “Saboda haka kada ku ji tsoronsu. Ba abin da yake a rufe da ba za a tone ba, ko kuwa a ɓoye da ba za a bayyana ba.
27. Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki.
28. Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yǎ hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.
29. Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa da yardar Ubanku.
30. Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su.
31. Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.
32. “Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama.
33. Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.
34. “Kada fa ku ɗauka na zo ne don in kawo salama a duniya. Aʼa, ban zo don in kawo salama ba, sai dai takobi.
35. Gama na zo ne in sa, “ ‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa, ʼya da mahaifiyarta, matar ɗa da surukarta— 
36. abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’
37. “Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yǎ zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yǎ zama nawa ba;
38. duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yǎ zama nawa ba.
39. Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi.
40. “Wanda ya karɓe ku, ya karɓe ni ne, wanda kuma ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.
41. Duk wanda ya karɓi annabi don shi annabi ne, zai sami ladar annabi, duk kuwa wanda ya karɓi mutum mai adalci don shi mai adalci ne, zai sami ladar mai adalci.
42. In kuma wani ya ba wa ɗaya daga cikin ƙananan nan ko da kwaf ruwan sanyi ne kan shi almajirina ne, gaskiya nake gaya muku, ba shakka ba zai rasa ladarsa ba.”