A A A A A

Mattiyu 10:1-20
1. Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
2. Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu: da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗanʼuwansa Andarawus; Yaƙub ɗan Zebedi da ɗanʼuwansa Yohanna;
3. Filibus da Bartolomeyu; Toma da Mattiyu mai karɓar haraji; Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus;
4. Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.
5. Waɗannan sha biyun ne Yesu ya aika da umarni cewa: “Kada ku je cikin Alʼummai, ko kuwa ku shiga wani garin Samariyawa.
6. A maimakon haka ku je wajen ɓatattun tumakin Israʼila.
7. Saʼad da kuke tafiya, ku yi waʼazi, kuna cewa: ‘Mulkin sama ya kusato.’
8. Ku warkar da marasa lafiya, ku ta da matattu, ku tsabtace kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.
9. Kada ku riƙe wata zinariya ko azurfa ko jan ƙarfe a aljihunanku;
10. kada ku ɗauki jaka don tafiya, ko ƙarin riga, ko takalma ko sanda; domin maʼaikaci ya cancanci hakkinsa.
11. “Kowane gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a wurin, ku kuma zauna a gidansa har sai kun tashi.
12. Da shigarku gidan, ku yi gaisuwa.
13. In gidan na kirki ne, bari salamarku ta zauna a kansa; in kuwa ba mai kirki ba, salamarku ta komo muku.
14. Duk wanda ya ƙi marabtarku ko ya ƙi sauraron kalmominku, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku saʼad da kuka fita gidan ko garin.
15. Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shariʼa fiye da wannan gari.
16. Ina aikanku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.
17. “Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majamiʼunsu.
18. Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Alʼummai.
19. Amma saʼad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa,
20. gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.