A A A A A

Mattiyu 9:18-38
18. Yayinda yake faɗin wannan, sai wani mai mulki ya zo ya durƙusa a gabansa, ya ce, “Yanzu yanzun nan diyata ta rasu. Amma ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, za ta kuwa rayu.”
19. Yesu ya tashi ya tafi tare da shi, haka ma almajiransa.
20. A daidai wannan lokaci sa ga wata mace wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini ta raɓo ta bayansa ta taɓa gefen rigarsa.
21. Ta ce a ranta, “Ko da rigarsa ce kawai na taɓo, zan warke.”
22. Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, “Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke,” Nan take macen ta warke.
23. Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya,
24. sai ya ce, “Ku ba da wuri. Ai, yarinyar ba ta mutu ba, tana barci ne.” Amma suka yi masa dariya.
25. Bayan an fitar da taron waje, sai ya shiga ciki ya kama yarinyar a hannu, ta kuwa tashi.
26. Labarin wannan kuwa ya bazu koʼina a yankin.
27. Da Yesu ya fita daga can, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna kira, suna cewa, “Ka yi mana jinƙai, Ɗan Dawuda!”
28. Da ya shiga cikin gida, sai makafin nan suka zo wurinsa, ya kuma tambaye su, “Kun gaskata cewa ina iya yin wannan?” Suka amsa suka ce, “I, Ubangiji.”
29. Saʼan nan ya taɓa idanunsu ya ce, “Bisa ga bangaskiyarku a yi muku haka”;
30. sai idanunsu suka buɗe. Yesu ya gargaɗe su sosai ya ce, “Ku lura kada wani yǎ san wani abu game da wannan.”
31. Amma suka fita suka yi ta baza labari game da shi koʼina a wannan yankin.
32. Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana.
33. Saʼad da aka fitar da aljanin kuwa, sai beben ya yi magana. Taron suka yi mamaki suka ce, “Ba a taɓa ganin irin wannan abu a Israʼila ba.”
34. Amma Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”
35. Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majamiʼunsu, yana waʼazin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
36. Da ya ga taron mutane, sai ya ji tausayinsu, domin an wulaƙanta su ba su kuma da mai taimako, kamar tumaki marasa makiyayi.
37. Sai ya ce wa almajiransa, “Girbi yana da yawa, amma maʼaikata kaɗan ne.
38. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yǎ aiko da maʼaikata cikin gonarsa na girbi.”