English
A A A A A

Mattiyu 9:1-17
1. Yesu ya shiga jirgin ruwa, ya ƙetare ya zo garinsa.
2. Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu ɗana, an gafarta maka zunubanka.”
3. Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, “Wannan mutum yana yin saɓo!”
4. Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, “Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku?
5. Wanne ya fi sauƙi: a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’
6. Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yǎ gafarta zunubai....” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”
7. Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida.
8. Da taron suka ga haka, sai suka cika da tsoro, suka yabi Allah wanda ya ba wa mutane irin ikon nan.
9. Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.
10. Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma “masu zunubi” suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa.
11. Saʼad da Farisiyawa suka ga haka, sai suka tambayi almajiransa suka ce, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji, da ‘masu zunubi’?”
12. Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya.
13. Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi: ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’ Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”
14. Sai almajiran Yohanna suka zo suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa mu da Farisiyawa muke azumi, amma almajiranka ba sa yi?”
15. Yesu ya amsa, ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, saʼan nan za su yi azumi.
16. “Ba mai yin faci da sabon ƙyalle a kan tsohuwar riga, gama facin zai kece rigar yǎ sa kecewar ma ta fi ta dā muni.
17. Mutane kuma ba sa zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In suka yi haka, salkunan za su farfashe, ruwan inabin kuwa yǎ zube salkunan kuma su lalace. Aʼa, ai, sukan zuba sabon ruwan inabi ne a cikin sababbin salkuna, don a kiyaye dukan biyun.”