A A A A A

Mattiyu 8:18-34
18. Da Yesu ya ga taron mutane kewaye da shi, sai ya ba da umarni a ƙetare zuwa ɗayan hayin tafkin.
19. Sai wani malamin dokoki ya zo wurinsa ya ce, “Malam, zan bi ka duk inda za ka.”
20. Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama kuma suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”
21. Sai wani almajiri ya ce masa, “Ubangiji, da farko bari in je in binne mahaifina.”
22. Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.”
23. Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi.
24. Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.
25. Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”
26. Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Saʼan nan ya tashi ya tsauta wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.
27. Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”
28. Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya.
29. Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yǎ yi?
30. Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo.
31. Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.”
32. Ya ce musu, “Ku tafi!” Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa.
33. Masu kiwon aladun suka ruga, suka je cikin gari suka ba da labarin dukan wannan, haɗe da abin da ya faru da mutanen nan masu aljanu.
34. Sai dukan garin suka fito don su taryi Yesu. Da suka kuwa gan shi, sai suka roƙe shi yǎ bar musu yanki.