A A A A A

Mattiyu 8:1-17
1. Da ya sauko daga gefen dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi.
2. Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtace ni.”
3. Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtace!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa.
4. Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.”
5. Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani jarumi ya zo wurinsa, yana neman taimako.
6. Ya ce, “Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai.”
7. Yesu ya ce masa, “Zan je in warkar da shi.”
8. Jarumin ya amsa, “Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke.
9. Gama ni kaina mutum ne a ƙarƙashin iko, da kuma sojoji a ƙarƙashina. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yǎ tafi; wancan kuma, ‘Zo nan,’ sai yǎ zo. Nakan ce wa bawana, ‘Yi wannan,’ sai kuwa yǎ yi.”
10. Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, “Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Israʼila da bangaskiya mai girma haka ba.
11. Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama.
12. Amma za a jefar da ʼyaʼyan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”
13. Saʼan nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.
14. Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi.
15. Ya taɓa hannunta sai zazzaɓin ya sake ta, ta kuwa tashi ta fara yin masa hidima.
16. Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.
17. Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa: “Ya ɗebi rashin lafiyarmu, ya kuma ɗauki cututtukarmu.”