English
A A A A A

Afisawa 2:1-22
1. A dā, ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku.
2. Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya da Shaiɗan, wannan mai mulkin sararin sama. Shi ne ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙi biyayya ga Allah.
3. Dukanmu mun yi irin rayuwan nan a dā, muna bin kwaɗayi da shaʼawace shaʼawacen jikunanmu da tunaninmu. Mun ba wa Allah haushi, kuma dā za a hukunta mu kamar sauran mutane.
4. Amma saboda yawan ƙaunar da yake yi mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai,
5. ya ba mu rai saʼad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.
6. Allah ya tashe mu tare da Kiristi ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya.
7. Allah ya yi haka domin a zamanai masu zuwa yǎ yi amfani da mu a matsayin yalwar alherinsa da ya wuce misali, yadda yake a dukan abin da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu.
8. Allah ya cece ku ta wurin alheri saʼad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yin ku ba ne, kyauta ce daga Allah.
9. Ceto ba lada ba ne saboda abubuwa masu kyau da muka yi, don kada wani yǎ yi taƙama.
10. Allah ya shirya mana mu yi abubuwa masu kyau mu kuma yi rayuwa kamar yadda kullum yake so mu yi. Shi ya sa ya aiko da Kiristi yǎ sa mu zama abin da muke.
11. Kada ku manta cewa dā ku Alʼummai ne. A gaskiya ma, a dā masu kira kansu “masu kaciya,” suna ce da ku “marasa kaciya” (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannun mutum).
12. A lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Israʼila, kuma ba ku da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah.
13. Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi.
14. Gama shi da kansa ne ya kawo salama a tsakanin Yahudawa da Alʼummai wanda ya mai da biyu nan suka zama ɗaya, ya rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu.
15. Kiristi ya ba da jikinsa don yǎ kawar da doka da dukan umarnanta da ƙaʼidodinta. Ya yi haka domin yǎ halicci sabuwar zuriya daga zuriyan nan biyu. Ta haka kuma yǎ kawo salama tsakaninsu.
16. A kan gicciye Kiristi ya kawar da ƙiyayyar da take tsakaninmu da juna. Ya kuma kawo salama tsakaninmu da Allah.
17. Ya zo ya yi muku waʼazin salama; ku da kuke nesa da shi, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa.
18. Gama ta wurinsa dukanmu za mu iya zuwa gun Uba ta wurin Ruhu guda.
19. Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ʼyan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma.
20. Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci.
21. Shi ne yake riƙe dukan ginin a haɗe yake kuma sa yǎ yi girma yǎ zama haikali mai tsarki domin Ubangiji.
22. Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.