English
A A A A A

Afisawa 1:1-23
1. Wasiƙa daga Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yǎ zama manzon Kiristi Yesu. Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa, da suke amintattu cikin Kiristi Yesu:
2. Bari alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi su kasance tare da ku.
3. Yabo ya tabbata ga Allah da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama.
4. Tun dā can, kafin ma a halicci duniya Allah ya zaɓe mu a cikin Kiristi don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa.
5. A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu mu zama ʼyaʼyansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu. Wannan kuwa ya sa ya ji daɗi.
6. Don haka muna yabon Allah saboda alherin da ya yi mana domin mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.
7. Ta wurin mutuwar Kiristi ne muka sami ʼyanci, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah
8. wanda ya ba mu ba iyaka tare da dukan hikima da fahimta.
9. Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yǎ cika ta wurin Kiristi.
10. Saʼan nan da lokaci ya yi, Allah zai yi duk abin da ya shirya, kuma Kiristi zai kawo kome da yake a sama da ƙasa a ƙarƙashin ikonsa.
11. Saboda Kiristi ne muka sami gādo daga Allah, gama ya zaɓe mu daga farko, kome kuma ya faru yadda ya shirya tuntuni.
12. Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi ne, za mu yabi ɗaukakar Allah.
13. Kiristi ya kawo muku gaskiya, wadda take labari mai daɗi game da yadda za ku sami ceto. Kun sa bangaskiyarku a cikin Kiristi aka kuwa yi muku alkawarin Ruhu Mai Tsarki don a nuna ku na Allah ne.
14. Ruhu Mai Tsarki shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari kuma cewa mu mallakarsa ce. Wannan shi ne wani dalilin da za mu yabi Allahnmu mai ɗaukaka.
15. Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan tsarkaka,
16. ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin adduʼoʼina.
17. Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai ɗaukaka, yǎ ba ku Ruhunsa. Ruhun kuwa zai ba ku hikima yǎ kuma sa ku gane abin da ake nufi da sanin Allah.
18. Ina kuma adduʼa cewa zuciyarku ta waye don ku gane begen da aka ba ku saʼad da Allah ya zaɓe ku. Saʼan nan ne za ku gane albarku masu ɗaukakan da za su zama naku tare da dukan tsarkaka.
19. Ina so ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali wanda yake namu. Da wannan ikon nan mai girma ne
20. ya ta da Kiristi daga matattu ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya.
21. Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta da iko da ƙarfi da mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa.
22. Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi wannan iko a kan kome don amfanin ikkilisiya.
23. Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya.