A A A A A

Ayyukan Manzanni 8:26-40
26. To wani malaʼikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Ka yi kudu zuwa hanyar-hanyar hamada-da ta gangara daga Urushalima zuwa Gaza.”
27. Saboda haka ya kama hanya, a kan hanyarsa kuwa sai ya sadu da wani mutumin Itiyofiya, wanda yake bābā, hafsa mai muhimmanci wanda yake lura da dukan maʼajin Kandas, sarauniyar mutanen Itiyofiya. Mutumin nan ya tafi Urushalima ne domin yin sujada,
28. a kan hanyarsa ta komawa gida kuwa yana zaune bisan karusarsa yana karatun littafin annabin Ishaya.
29. Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa wurin karusan nan ka yi kusa da ita.”
30. Sai Filibus ya ruga zuwa wajen karusar ya kuma ji mutumin yana karatun littafin annabin Ishaya. Filibus ya yi tambaya, ya ce, “Ka fahimci abin da kake karantawa?”
31. Sai ya ce, “Ina fa zan iya, in ba dai wani ya fassara mini ba?” Saboda haka sai ya gayyaci Filibus yǎ hau yǎ zauna tare da shi.
32. Bābān yana karanta wannan Nassin: “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka, kuma kamar ɗan rago a hannun mai askin gashinsa yake shiru, haka kuwa bai buɗe bakinsa ba.
33. A cikin wulakacinnsa aka hana masa gaskiya. Wa zai iya yin zancen zuriyarsa? Gama an ɗauke ransa daga duniya.”
34. Sai bābān ya tambayi Filibus ya ce, “Ka gaya mini, ina roƙonka, annabin yana magana a kan wane ne, kansa ne, ko kuwa wani dabam?”
35. Saʼan nan Filibus ya fara da wannan Nassi ɗin ya kuma fada masa labari mai daɗi game da Yesu.
36. Yayinda suke cikin tafiya a kan hanya, sai suka iso wani wurin ruwa bābān nan ya ce, “Duba, ga ruwa. Me zai hana a yi mini baftisma?”
37. ***
38. Ya kuwa ba da umarni a tsai da karusar. Saʼan nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma.
39. Saʼad da suka fita daga cikin ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, bābān kuwa bai ƙara ganinsa ba, amma ya ci gaba da tafiyarsa yana farin ciki.
40. Filibus kuwa ya fito a Azotus, ya yi ta zagawa, yana waʼazin bishara a dukan garuruwan sai da ya kai Kaisariya.