A A A A A

Yohanna 4:31-54
31. Ana cikin haka almajiransa kuwa suka roƙe shi suka ce, “Rabbi, ci wani abu.”
32. Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku sani ba.”
33. Sai almajiran suka ce wa juna, “Shin, ko wani ya kawo masa abinci ne?”
34. Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.
35. Ba kukan ce, ‘Sauran wata huɗu a yi girbi ba?’ Ina gaya muku, ku buɗe idanunku ku dubi gonaki! Sun isa girbi.
36. Ko yanzu ma mai girbi yana samun ladansa, ko yanzu ma yana girbin amfani domin rai madawwami, saboda mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.
37. Karin maganan nan gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani kuma da girbi.’
38. Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.”
39. Samariyawa da yawa daga wannan gari suka gaskata da shi saboda shaidar macen da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.”
40. To, da Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roƙe shi yǎ zauna da su, ya kuwa zauna kwana biyu.
41. Saboda kalmominsa kuwa da yawa suka gaskata.
42. Sai suka ce wa macen, “Yanzu kam mun gaskata, ba don abin da kika faɗa kawai ba; yanzu mun ji da kanmu, mun kuwa san cewa wannan mutum tabbatacce shi ne Mai Ceton duniya.”
43. Bayan kwana biyun nan sai ya bar can zuwa Galili.
44. (To, Yesu kansa ya taɓa faɗa cewa annabi ba shi da daraja a ƙasarsa).
45. Da ya isa Galili, sai mutanen Galili suka marabce shi. Sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin Bikin Ƙetarewa, gama su ma sun kasance a can.
46. Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani maʼaikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum.
47. Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yǎ zo yǎ warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa.
48. Yesu ya ce masa, “Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”
49. Maʼaikacin hukuman ya ce, “Ranka yǎ daɗe, ka zo kafin ɗana yǎ mutu.”
50. Sai Yesu ya amsa, ya ce, “Ka tafi. Ɗanka zai rayu.” Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi.
51. Tun yana kan hanya, bayinsa suka tarye shi da labari cewa yaron yana warkewa.
52. Da ya tambayi lokacin da ɗansa ya sami sauƙi, sai suka ce masa, “Zazzaɓin ya sake shi jiya a saʼa ta bakwai.”
53. Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, “Ɗanka zai rayu.” Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata.
54. Wannan ce abin banmamaki ta biyu da Yesu ya yi, bayan zuwansa daga Yahudiya zuwa Galili.