Instagram
English
A A A A A
Baibul a cikin shekara guda
Afrilu 21

Mahukunta 7:1-25
1. Sai Yerubba'al, wato Gidiyon, da mutanen da suke tare da shi suka yi sammako, suka kafa sansaninsu kusa da maɓuɓɓugan Harod. Madayanawa kuwa suka kafa sansaninsu a arewa da su, kusa da tudun More a kwarin.
2. Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Mutanen da suke tare da kai sun yi yawa da zan ba da Madayanawa a hannunsu, kada ya zama Isra'ilawa su yi mini fāriya, su ce, ‘Ƙarfinmu ne ya cece mu.’
3. Yanzu sai ka ce wa mutanen, ‘Duk mai jin tsoro da mai rawar jiki, ya koma gida!’ ” Da Gidiyon ya gwada su, mutum dubu ashirin da biyu (22,000) suka koma, dubu goma (10,000) suka tsaya.
4. Ubangiji ya ce wa Gidiyon, “Har yanzu mutanen sun yi yawa. Ka kai su bakin rafi domin in jarraba maka su a can. Wanda na faɗa maka shi zai tafi tare da kai, to, shi ne zai tafi, wanda kuma na faɗa ba zai tafi tare da kai ba, to, ba zai tafi ba.”
5. Gidiyon ya kai mutanen bakin rafi, Ubangiji kuwa ya ce wa Gidiyon, “Duk wanda ya tanɗi ruwa kamar kare, sai ka ware shi waje ɗaya. Wanda kuma ya durƙusa ya sha ruwa, ka ware shi waje ɗaya.”
6. Yawan waɗanda suka tanɗi ruwa su ɗari uku ne. Sauran mutane duka kuwa sun durƙusa ne suka sha ruwan.
7. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Gidiyon, “Da mutum ɗari uku ɗin nan da suka tanɗi ruwa zan cece ku. Zan ba da Madayanawa a gare ku, ka sallami sauran, kowa ya koma gidansa.”
8. Mutane suka ɗauki guzuri da ƙahoni, Gidiyon kuwa ya sallami sauran mutane, amma ya bar mutum ɗari uku ɗin nan. Sansanin Madayanawa kuwa yana ƙasa da su a kwarin.
9. A wannan dare sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi, ka tafi sansanin Madayanawa, gama na ba da su gare ka.
10. Amma idan kana jin tsoro ka tafi kai kaɗai, ka tafi tare da Fura, baranka.
11. Za ka ji abin da suke cewa. Bayan haka za ka sami ƙarfin hali da za ka tafi ka fāda wa sansaninsu.” Gidiyon kuwa ya tafi tare da Fura baransa a gefen sansanin abokan gāba.
12. Madayanawa, da Amalekawa, da mutanen gabas duka suna nan da yawa a shimfiɗe cikin kwarin, kamar fara. Raƙumansu kuma suna da yawa kamar yashi a bakin teku. Ba wanda zai iya ƙidaya su.
13. Sa'ad da Gidiyon ya tafi, sai ya ji wani yana faɗa wa abokinsa mafarkin da ya yi. Ya ce, “Na yi mafarki, na ga wainar sha'ir ta faɗo a tsakiyar sansaninmu. Ta zo ta bugi alfarwa. Alfarwar kuwa ta fāɗi rigingine.”
14. Abokinsa ya amsa, ya ce, “Ai, ba wani abu ba ne. Wannan takobin Gidiyon ne, ɗan Yowash. Ba'isra'ile! Allah ya ba shi nasara kan Madayanawa da dukan rundunanmu!”
15. Da Gidiyon ya ji mafarkin, har da fassarar, sai ya yi sujada, ya koma a sansaninsu na Isra'ilawa. Da ya isa, sai ya ce, “Ku tashi, gama Ubangiji ya ba da rundunar Madayanawa a gare ku.”
16. Sai ya raba mutum ɗari uku ɗin kashi uku, ya ba kowannensu ƙaho, da tulu, da jiniya a cikin tulun.
17. Sa'an nan ya ce musu, “Sa'ad da muka kai sansani, sai ku dube ni, ku yi duk abin da nake yi. Yadda na yi, ku ma ku yi haka.
18. Sa'ad da ni da dukan waɗanda suke tare da ni muka busa ƙahoni, sai ku kuma ku busa ƙahonin a kowane gefen sansani, sa'an nan ku yi ihu, ku ce, ‘Ubangiji da Gidiyon!’ ”
19. Gidiyon da mutum ɗari da suke tare da shi, suka kai gefen sansanin wajen tsakiyar dare, bayan an sauya matsara. Sai suka busa ƙahonin, suka fasa tulunan da suke a hannuwansu.
20. Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka riƙe jiniyoyi a cikin hannuwansu na hagu, da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama. Sai suka yi kuwa, suka ce, “Takobin Ubangiji da na Gidiyon!”
21. Kowannensu ya yi tsaye a inda yake kewaye da sansanin. Dukan rundunar Madayanawa kuwa suka gudu, suna ihu.
22. Da suka busa ƙahonin nan ɗari uku, sai Ubangiji ya sa Madayanawa suka yi ta sassare junansu da takuba. Suka gudu zuwa Zerera har Bet-shitta, har kuma zuwa garin Abel-mehola, kusa da Tabbat.
23. Jama'ar kabilar Naftali, da Ashiru, da Manassa, suka ji kira, suka fito, suka runtumi Madayanawa.
24. Gidiyon kuma ya aika a dukan ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce musu, “Ku gangaro, ku yaƙi Madayanawa, ku tare mashigan Kogin Urdun da rafuffuka, har zuwa Bet-bara.” Aka kuwa kira dukan Ifraimawa, su kuwa suka hana wa Madayanawa mashigan Kogin Urdun da rafuffuka, har zuwa Bet-bara.
25. Suka kama sarakunan Madayanawa biyu, Oreb da Ziyib. Suka kashe Oreb a kan dutsen Oreb, Ziyib kuwa suka kashe shi a wurin matsewar ruwan inabi na Ziyib a lokacin da suke runtumar Madayanawa. Sai suka kawo wa Gidiyon kan Oreb da na Ziyib a inda yake a gabashin Urdun.

Mahukunta 8:1-35
1. Mutanen Ifraimu suka ce wa Gidiyon, “Me ke nan ka yi mana, da ba ka kirawo mu lokacin da ka tafi yaƙi da Madayanawa ba?” Suka yi masa gunaguni ƙwarai.
2. Amma ya ce musu, “Yanzu, me na yi fiye da ku? Ai, kalar inabin Ifraimu ta fi dukan girbin Abiyezer, wato ɗan abin da kuka yi ya fi wanda kabilata ta yi nesa.
3. Ga shi, Allah ya ba da Oreb da Ziyib sarakunan Madayanawa a gare ku. To, me na yi wanda ya fi naku?” Da ya faɗi haka, sai suka huce.
4. Da Gidiyon ya zo Urdun sai ya haye tare da mutum ɗari uku ɗin nan da suke tare da shi. Ko da yake sun gaji, duk da haka suka yi ta runtumar magabta.
5. Gidiyon ya ce wa mutanen Sukkot, “Ina roƙonku, ku ba mutanen da suke tare da ni abinci, gama sun gaji, ga shi kuwa, ina runtumar Zeba da Zalmunna, sarakunan Madayanawa.”
6. Shugabannin Sukkot kuwa suka ce, “Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka abinci?”
7. Gidiyon ya ce, “To, sa'ad da Ubangiji ya ba da Zeba da Zalmunna a hannuna, zan tsattsaga jikinku da ƙayayuwan jeji.”
8. Daga can ya tafi Feniyel, ya roƙe su yadda ya roƙi mutanen Sukkot. Mutanen Feniyel kuma suka amsa masa daidai yadda mutanen Sukkot suka amsa masa.
9. Sai Gidiyon ya ce wa mutanen Feniyel, “Sa'ad da na dawo cikin salama, zan rushe wannan hasumiya.”
10. Zeba da Zalmunna kuwa suna Karkor tare da rundunarsu, mutum wajen dubu goma sha biyar (15,000), waɗanda suka ragu daga cikin rundunar mutanen gabas, gama an kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000), masu takuba.
11. Gidiyon kuwa ya bi ta hanyar gefen hamada wadda take gabas da Noba da Yogbeha, ya faɗa wa rundunar, ta yadda ba su zato.
12. Zeba da Zalmunna, sarakunan nan biyu na Madayana suka gudu, amma ya bi su, ya kamo su. Ya sa dukan rundunarsu ta gigice.
13. Sa'an nan Gidiyon, ɗan Yowash, ya komo daga yaƙin ta hanyar hawan Heres.
14. Gidiyon ya kama wani saurayi na Sukkot, ya yi masa tambayoyi. Shi kuwa ya rubuta masa sunayen sarakuna da na dattawan Sukkot, mutum saba'in da bakwai.
15. Sa'an nan ya zo wurin mutanen Sukkot ya ce musu, “To, ga Zeba da Zalmunna waɗanda kuka yi mini ba'a saboda su, kuna cewa, ‘Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka da suka gaji abinci?’ To, ga su!”
16. Ya kama dattawan garin Sukkot ya hukunta su da ƙayayuwa.
17. Ya kuma rushe hasumiyar Feniyel, ya karkashe mutanen birnin.
18. Sa'an nan ya ce wa Zeba da Zalmunna, “Waɗanne irin mutane ne kuka kashe a Tabor?” Suka amsa, “Kamar yadda kake, haka suke. Suna kama da 'ya'yan sarki.”
19. Gidiyon ya ce musu, “Su 'yan'uwana ne, mahaifiyarmu ɗaya. Da ba ku kashe su ba, da ba zan kashe ku ba.”
20. Ya ce wa Yeter, ɗan farinsa, “Tashi, ka kashe su.” Amma saurayin bai zare takobinsa ba, gama yana jin tsoro domin shi yaro ne.
21. Sai Zeba da Zalmunna suka ce, “Tashi da kanka, ka kashe mu, gama yadda mutum yake haka kuma ƙarfinsa yake.” Gidiyon kuwa ya tashi ya kashe Zeba da Zalmunna. Ya kwance kayan ado daga wuyan raƙumansu.
22. Sa'an nan mutanen Isra'ila suka ce wa Gidiyon, “Ka yi mulkinmu, kai da 'ya'yanka, da jikokinka, gama ka cece mu daga hannun Madayanawa.”
23. Gidiyon ya ce musu, “Ba zan yi mulkinku ba, ɗana kuma ba zai yi mulkinku ba, Ubangiji ne zai yi mulkinku.”
24. Ya ci gaba ya ce, “Ina roƙon kowannenku ya ba ni 'yan kunne daga cikin ganimar da ya kwaso.” (Gama Madayanawa suna da 'yan kunne na zinariya, gama su mutanen hamada ne.)
25. Suka ce, “Lalle, za mu ba ka su.” Nan da nan suka shimfiɗa mayafi, kowa ya zuba 'yan kunnen da ya kwaso ganima.
26. Nauyin 'yan kunnen zinariya da ya roƙa ya kai shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), banda kayan ado, da na rataye-rataye, da tufafin shunayya waɗanda sarakunan Madayanawa suke sawa, banda ɗan gaba da yake a wuyan raƙumansu.
27. Gidiyon kuwa ya yi gunki da zinariyar, ya ajiye a birninsa, wato Ofra. Isra'ilawa kuma suka bar bin Allah, suka tafi can domin su yi wa gunkin sujada, ya zama tarko ga Gidiyon da iyalinsa.
28. Da haka Isra'ilawa suka mallaki Madayanawa har ba su zamar musu barazana ba. Ƙasar kuwa ta zauna lafiya shekara arba'in a zamanin Gidiyon.
29. Gidiyon kuwa ya tafi ya zauna a gidansa na kansa.
30. Yana kuma da 'ya'ya maza saba'in, gama yana da mata da yawa.
31. Yana kuma da ƙwarƙwara wadda take a Shekem, ta haifi masa ɗa, ya sa masa suna Abimelek.
32. Sa'an nan Gidiyon, ɗan Yowash, ya rasu da kyakkyawan tsufa. Aka binne shi a kabarin Yowash mahaifinsa, a Ofra, birnin kabilar Abiyezer.
33. Bayan rasuwar Gidiyon, sai Isra'ilawa suka sāke yin rashin aminci ga Allah, suka yi wa Ba'al sujada. Suka yi Ba'al-berit ya zama allahnsu.
34. Suka daina bauta wa Ubangiji Allahnsu, wanda ya cece su daga magabtan da suke kewaye da su.
35. Ba su kuwa sāka wa iyalin Gidiyon da alheri ba, saboda dukan alherin da ya yi wa Isra'ilawa.

Zabura 49:10-20
10. Yakan sa masu hikima su ma su mutu, Haka nan ma wawaye da mutanen banza, Za su mutu su bar dukiyarsu ga zuriyarsu.
11. Kaburburansu za su zama gidajensu har abada, Can za su kasance kullum, Ko da yake a dā suna da ƙasa ta kansu.
12. Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba, Zai mutu kamar dabba.
13. Dubi abin da zai faru ga waɗanda suke dogara ga kansu, Da irin ƙaddarar waɗanda dukiya ta ishe su.
14. Za a ƙaddara su ga mutuwa kamar tumaki, Mutuwa ce za ta yi kiwonsu. Da safe adalai za su ci nasara a kansu, Sa'ad da gawawwakinsu suke ruɓewa a ƙasar matattu, Nesa da gidajensu.
15. Amma Allah zai fanshe ni, Zai ɗauke ni daga ikon mutuwa.
16. Kada ka damu sa'ad da mutum ya zama attajiri, Ko kuwa dukiyarsa ta ƙasaita,
17. Domin ba zai ɗauke ta a lokacin mutuwarsa ba, Dukiyarsa ba za ta shiga kabari tare da shi ba.
18. Ko da a ce mutum ya sami falalar wannan rai, Ana kuwa ta yabonsa saboda nasarar da ya ci,
19. Duk da haka zai tarar da kakanninsa waɗanda suka mutu, Inda duhu ya dawwama har abada.
20. Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba, Zai mutu kamar dabba.

Karin Magana 14:22-24
22. Waɗansu za su amince da kai, su girmama ka, idan ka aikata nagarta, idan kuwa ka aikata mugunta, to, ka yi babban kuskure.
23. Idan ka yi aiki za ka sami abin masarufi, idan kuwa ka zauna kana ta surutu kawai za ka zama matalauci.
24. Mutane masu hikima za a sāka musu da wadata, amma za a san wawa ta wurin wautarsa.

Luka 15:11-32
11. Ya kuma ce, “An yi wani mutum mai 'ya'ya biyu maza.
12. Sai ƙaramin ya ce wa ubansa, ‘Baba, ba ni rabona na gādo.’ Sai uban ya raba musu dukiyarsa.
13. Bayan 'yan kwanaki kaɗan sai ƙaramin ya tattara duk mallakarsa, ya kama hanya zuwa ƙasa mai nisa. A can ya fallasar da kayansa a wajen masha'a.
14. Da ya ɓad da kome kakat, aka yi babbar yunwa a ƙasar, sai ya shiga fatara.
15. Ya je ya rāɓu da wani ɗan ƙasar, shi kuwa ya tura shi makiyayar kiwon alade.
16. Har ma ya so ya cika cikinsa da kwasfar da aladu suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu
17. Amma da ya tara hankalinsa sai ya ce, ‘Kaitona! Nawa ne daga cikin barorin ubana da suke da abinci, da yake kamar ƙasa a gare su! Ga ni a nan kuwa, yunwa tana kisana!
18. Zan tashi, in tafi gun ubana, in ce masa, “Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka.
19. Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin barorinka.” ’
20. Sai ya tashi, ya taho wurin ubansa. Amma tun yana daga nesa, sai ubansa ya hango shi, tausayi ya kama shi, ya yiwo gudu, ya rungume shi, ya yi ta sumbatarsa.
21. Sai kuma ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa Mai Sama zunubi, na kuma saɓa maka. Ban ma cancanci a ƙara kirana ɗanka ba.’
22. Amma uban ya ce wa bayinsa, ‘Maza ku kawo riga mafi kyau, ku sa masa. Ku sa masa zobe da takalma,
23. a kuma kawo kiwataccen ɗan maraƙin nan, a yanka, mu ci, mu yi murna.
24. Don ɗan nan nawa dā ya mutu ne, amma a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma a yanzu an same shi.’ Sai suka yi ta farin ciki.
25. “A sa'an nan kuwa, babban ɗansa yana gona. Yana dawowa, ya yi kusa da gida ke nan, sai ya ji ana kaɗe-kaɗe da raye-raye.
26. Sai ya kira wani baran gidan, ya tambayi dalilin wannan abu.
27. Shi kuwa ya ce masa, ‘Ai, ɗan'uwanka ne ya dawo, tsohonku ya yanka kiwataccen ɗan maraƙin nan saboda ya sadu da shi lafiya ƙalau.’
28. Amma wan ya yi fushi, ya ƙi shiga. Ubansa kuwa ya fito, ya yi ta rarrashinsa.
29. Amma ya amsa wa ubansa ya ce, ‘Dubi yawan shekarun nan da na bauta maka. Ban taɓa ta da umarninka ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan taure ba, da za mu yi shagali tare da abokaina.
30. Amma da ɗan nan naka ya zo, wanda ya fallasar da dukiyarka a kan karuwai, ga shi, ka yanka masa kiwataccen ɗan maraƙin nan!’
31. Sai uban ya ce masa, ‘Ya ɗana, ai, kullum kana tare da ni, duk abin da yake nawa naka ne.
32. Ai kuwa, daidai ne a yi ta murna da farin ciki, don ɗan'uwan nan naka dā ya mutu, a yanzu ya komo, dā ya ɓata, amma an same shi.’ ”