A A A A A
Baibul a cikin shekara guda
Maris 1

Firistoci 26:1-46
1. Ubangiji ya ce, “Kada ku yi wa kanku gumaka, ko ku kafa sassaƙaƙƙiyar siffa, ko al'amudi. Kada kuma ku kafa wata siffa ta dutse a ƙasarku da za ku durƙusa mata, gama ni ne Ubangiji Allahnku.
2. Sai ku kiyaye lokatan sujadata, ku girmama alfarwa ta sujada. Ni ne Ubangiji.
3. “Idan kun bi dokokina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su,
4. sa'an nan zan ba da ruwan sama a lokacinsa, ƙasar kuwa za ta ba da albarkarta, itatuwan gonaki kuma za su ba da 'ya'yansu.
5. Za ku yi ta girbi, har lokacin tattara 'ya'yan inabi, za ku kuma yi ta tattara 'ya'yan inabi har zuwa lokacin shuka. Za ku ci abincinku, ku ƙoshi, ku yi zamanku a ƙasarku lafiya.
6. “Zan ba da salama cikin ƙasar. Za ku kwanta, ba abin da zai razana ku. Zan kawar da mugayen dabbobi daga ƙasar. Ba za a ƙara yin yaƙi a ƙasarku ba.
7. Za ku runtumi maƙiyanku, za su kuwa fāɗi ta kaifin takobi a gabanku.
8. Mutum biyar ɗinku za su runtumi mutum ɗari, mutum ɗari ɗinku za su runtumi mutum dubu goma. Maƙiyanku kuwa za su fāɗi a gabanku ta kaifin takobi.
9. Zan dube ku da idon rahama, in sa muku albarka, in riɓaɓɓanya ku. Zan tabbatar muku da alkawarina.
10. Za ku girbi amfani mai yawa har kun zubar da sūnā tukuna kafin ku sami wurin ajiye sabo.
11. Zan kafa wurin zamana a tsakiyarku, ba kuwa zan gaji da ku ba.
12. Zan yi tafiya tare daku, in zama Allahnku, ku kuma ku zama mutanena.
13. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, don kada ku zama bayinsu. Na karya ikonsu da yake danne ku, na bar ku ku yi tafiya a sake.”
14. “Amma idan ba za ku kasa kunne gare ni ba, to, za ku sha hukunci.
15. Idan kuma kuka yi watsi da dokokina, ba ku kuwa kula da ka'idodina ba, har kuka ƙi kiyaye umarnaina, kuka karya alkawarina,
16. to, zan hukunta ku. Zan aukar muku da bala'i, da cuce-cuce da ba su warkuwa, da zazzaɓin da zai lalatar muku da ido, rai zai zama muku da wahala. Za ku yi shuka a banza gama maƙiyanku ne za su ci.
17. Zan yi gāba da ku in sa maƙiyanku su ɗibge ku, waɗanda suke ƙinku za su mallake ku. Za ku yi ta gudu ba mai korarku.
18. “Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in tsananta hukuncinku har sau bakwai saboda zunubanku.
19. Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma ta zama kamar tagulla.
20. Za ku ɓarnatar da ƙarfinku a banza gama ƙasarku ba za ta ba da amfaninta ba, itatuwan ƙasar kuma ba za su ba da 'ya'ya ba.
21. “Idan har yanzu kuka tayar mini, ba ku kasa kunne gare ni ba, sai in ƙara yawan hukuncinku har sau bakwai, saboda zunubanku.
22. Zan kuwa turo muku mugayen namomin jeji waɗanda za su kashe 'ya'yanku, su hallakar da dabbobinku, su sa ku zama kaɗan, har ba mai gilmayya a hanyoyinku.
23. “Idan wannan hukunci bai sa kun juyo gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini,
24. sai in hau ku da hukunci, har ya fi na dā riɓi bakwai saboda zunubanku.
25. Zan sa a kawo muku yaƙi saboda karya alkawarina da kuka yi. Idan kuwa kun tattaru a cikin biranenku, sai in aukar muku da masifa, in bashe ku ga maƙiyanku.
26. Zan katse abincinku, mata goma za su dafa abincinku a murhu ɗaya, su rarraba muku shi da ma'auni. Za ku ci, amma ba za ku ƙoshi ba.
27. “Amma idan duk da haka ba ku kasa kunne gare ni ba, amma kuka ci gaba da tayar mini,
28. sai ni ma in tayar muku da fushi, in hukunta ku har riɓi bakwai, saboda zunubanku.
29. Za ku ci naman 'ya'yanku mata da na 'ya'yanku maza.
30. Zan lalatar da masujadanku, in rurrushe bagaden ƙona turarenku, in jefar da gawawwakinku a kan gumakanku, raina kuwa zai ji ƙyamarku.
31. Zan sa biranenku su zama kangwaye, in mai da wuraren yin sujada kufai, ba zan shaƙi ƙanshin turarenku ba.
32. Ni zan lalatar da ƙasar har maƙiyanku da suke zaune a ciki za su yi mamaki.
33. Zan sa a kawo muku yaƙi a warwatsa ku a baƙin ƙasashe, ƙasarku za ta zama kufai, biranenku kuwa za su lalace.
34. Sa'an nan ƙasar za ta ji daɗin hutunta muddin tana zaune kango. Sa'ad da kuke a ƙasar maƙiyanku, ƙasar za ta huta, taji daɗin hutunta.
35. Muddin tana zaune kufai za ta sami hutawa, hutawa asabatan da ba ta samu ba a lokacin da kuke zaune cikinta.
36. “Amma ga waɗanda suka ragu, zan sa fargaba a zuciyarsu sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu. Ko motsin ganye kawai ma zai razanar da su su sheƙa a guje kamar waɗanda ake fafara da takobi, ga shi kuwa, ba mai korarsu, za su kuwa fāɗi.
37. Za su yi karo da juna kamar waɗanda suke tsere wa takobi, ko da yake ba wanda yake korarsu. Ba za su sami ikon tsaya wa maƙiyansu ba.
38. Za ku mutu a cikin al'ummai. Ƙasar maƙiyanku za ta haɗiye ku.
39. Sauranku da kuka ragu za ku lalace a ƙasashen maƙiyanku saboda muguntarku da ta kakanninku, za ku lalace kamarsu.
40. “Amma za su hurta muguntarsu da ta kakanninsu, da cin amana da suka yi mini, da kuma tayarwa da suka yi mini,
41. haka kuma ni na tayar musu, na kai su ƙasar maƙiyansu. Amma idan sun ƙasƙantar da kangararriyar zuciyarsu, suka tuba, suka bar muguntarsu,
42. sa'an nan zan tuna da alkawarina wanda na yi wa Yakubu, da Ishaku, da Ibrahim, zan kuwa tuna da ƙasar.
43. Amma za su fita daga ƙasar, ƙasar kuwa za ta ji daɗin hutunta muddin ba su ciki, tana zaman kango. Amma za su tuba saboda sun ƙi kula da ka'idodina, suka yi watsi da dokokina.
44. Duk da haka, sa'ad da suke a ƙasar maƙiyansu ba zan wulakanta su ba, ba kuwa zan ji ƙyamarsu, har da zan karya alkawarina da su ba, gama ni ne Ubangiji Allahnsu.
45. Amma saboda su zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu waɗanda na fisshe su daga ƙasar Masar a idon al'ummai domin in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.”
46. Waɗannan su ne dokoki, da ka'idodi, da umarnai waɗanda Ubangiji ya yi tsakaninsa da Isra'ilawa ta hannun Musa a bisa Dutsen Sinai.

Firistoci 27:1-34
1. Ubangiji ya ba Musa
2. waɗannan ka'idodi domin Isra'ilawa. Idan an ba da mutum ga Ubangiji don cikar babban wa'adi za a iya fansarsa ta wurin biya waɗannan kuɗi.
3. Abin da aka ƙayyade za su biya bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Masu biya Abin da za su biya Maza masu shekara 20-60 Shekel hamsin Mata masu shekara 20-60 Shekel talatin Maza masu shekara 5-20 Shekel ashirin Mata masu shekara 5-20 Shekel goma sha biyar Maza masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel biyar Mata masu wata guda zuwa shekara 5 Shekel uku Tsohon da ya fi shekara 60 Shekel goma sha biyar Tsohuwar da ta fi shekara 60 Shekel goma
4. ***
5. ***
6. ***
7. ***
8. Idan mutumin ya cika talauci har ya kasa biyan tamanin da aka kimanta, sai ya kawo mutumin da aka yi wa'adi a kansa a gaban firist, firist ɗin zai kimanta tamaninsa daidai da ƙarfin wanda ya yi wa'adin.
9. Idan kuwa dabba ce irin wadda mutane kan miƙa hadaya ga Ubangiji, dukan irin wannan da mutum yakan bayar ga Ubangiji zai zama tsattsarka.
10. Ba zai musaya shi da wani abu ba, ba zai musaya mai kyau da marar kyau, ko marar kyau da mai kyau ba. Idan kuwa ya musaya dabba da dabba, sai duka biyu, abar da aka musaya, da wadda aka musayar, za su zama tsarkakakku.
11. Idan kuwa dabbar marar tsarki ce, irin wadda ba a miƙa ta hadaya ga Ubangiji, sai mutumin ya kai dabbar a wurin firist.
12. Firist ɗin zai kimanta tamanin dabbar daidai darajarta, kamar yadda firist ya kimanta, haka zai zama.
13. Amma idan mutumin yana so ya fansa, sai ya yi ƙarin humushin tamanin da aka kimanta.
14. Idan mutum ya keɓe gidansa ga Ubangiji, sai firist ya kimanta tamanin gidan daidai darajarsa, ko gidan mai tsada ne, ko mai araha ne. Yadda shi firist ya kimanta tamaninsa, haka zai zama.
15. Idan shi wanda ya keɓe gida nasa yana so ya fansa, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin da aka kimanta, gidan kuwa zai zama nasa.
16. Idan mutum ya keɓe wa Ubangiji wani sashi daga cikin gonarsa ta gādo, sai ka kimanta tamanin gonar daidai da yawan irin da zai rafa. Gonar da za a yafa iri wajen garwa ashirin na sha'ir tamaninta zai zama wajen shekel hamsin.
17. Idan ya keɓe gonarsa daga shekara ta hamsin ta murna, ba za a rage kome daga cikin tamanin gonar da aka kimanta ba.
18. Amma idan ya keɓe ta bayan shekara ta hamsin ta murna, sai firist ya kimanta yawan kuɗin bisa ga yawan shekarun da suka ragu kafin shekara ta hamsin ta murna ta kewayo. Sai a rage kuɗin tamanin gonar.
19. Idan shi wanda ya keɓe gonar yana so ya fanshe ta, to, sai ya ƙara kashi ɗaya daga cikin biyar na tamanin kuɗin gonar, gonar kuwa za ta zama tasa.
20. Amma idan ba ya so ya fanshi gonar, ko kuwa ya riga ya sayar wa wani da gonar, faufau, ba zai sāke fansarta ba.
21. Sa'ad da aka mayar da gonar a shekara ta hamsin ta murna, za ta zama tsattsarka ta ubangiji kamar gonar da aka keɓe. Firist ne zai mallaka ta.
22. Idan kuwa ya keɓe wa Ubangiji gonar da ya saya, wadda ba ta gādo ba,
23. sai firist ya kimanta tamaninta har zuwa shekara ta hamsin ta murna. Shi mutumin zai ba da yawan abin da aka kimanta a ranar, abu mai tsarki ne ga Ubangiji.
24. A cikin shekara ta hamsin ta murna, sai a mayar da gonar ga wanda aka saye ta a hannunsa, wanda gonarsa ce ta gādo.
25. Sai a kimanta tamanin kowane abu bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi.
26. Kowane ɗan fari na dabba na Ubangiji ne, kada wani ya fanshi sa ko tunkiya, gama na Ubangiji ne.
27. Idan dabbar marar tsarki ce, sai mai ita ya kimanta tamanin kuɗinta, ya ƙara da humushin kuɗin, ya saya. Idan ba a fansa ba, sai a sayar bisa ga tamaninta.
28. Amma iyakar abin da mutum ya ba Ubangiji ɗungum daga cikin abubuwan da yake da su, ko mutum ko dabba, ko gonarsa ta gādo, ba za a sayar ko a fansar ba, gama kowane abu da aka keɓe mafi tsarki ne ga Ubangiji.
29. Ko da mutum ne aka ba Ubangiji ɗungum, ba za a fanshe shi ba, sai a kashe shi.
30. Dukan ushirin amfanin ƙasar, ko na hatsi ne, ko na 'ya'yan itatuwa ne, na Ubangiji ne, gama tsattsarka ne ga Ubangiji.
31. Idan wani yana so ya fanshi ushiri na kowane iri, sai ya ƙara humushin tamanin ushirin.
32. Dukan ushiri na shanu, da na tumaki da awaki, duk dai dabbar da ta zama ta goma bisa ga ƙirgar makiyayan, keɓaɓɓiya ce, ta Ubangiji ce.
33. Ba ruwan kowa da kyanta ko rashin kyanta. Kada kuma a musaya ta. Idan kuwa an musaya ta, sai dai su zama tsarkakakku ga Ubangiji, ita da abar da aka yi musayar. Ba za a fanshe su ba.
34. Waɗannan su ne umarnan da Ubangiji ya ba Musa a kan Dutsen Sinai saboda isra'ilawa.

Zabura 29:1-6
1. Ku yabi Ubangiji, ku alloli, Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa.
2. Ku yabi sunan Ubangiji mai daraja, Ku rusuna a gaban Mai Tsarki sa'ad da ya bayyana.
3. An ji muryar Ubangiji a kan tekuna, Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, Tsawar muryarsa kuwa ta yi amsa kuwa a bisa teku.
4. An ji muryar Ubangiji A dukan ikonsa da zatinsa!
5. Muryar Ubangiji takan karya itatuwan al'ul, Har ma da itatuwan al'ul na Lebanon.
6. Yakan sa duwatsun Lebanon su yi tsalle kamar 'yan maruƙa, Ya kuma sa Dutsen Harmon ya yi tsalle kamar ɗan maraƙi.

Karin Magana 10:22-25
22. Albarkar Ubangiji takan arzuta mutum, amma yawan aiki ba shi yake kawo arziki ba.
23. Wawa ne yake jin daɗin aikata mugunta, amma mai fasaha yana jin daɗin hikima.
24. Abin da mugun yake tsoro, shi yakan auko masa, amma adali yakan sami biyan bukatarsa.
25. Hadiri yakan taso ya wargaza mugaye, amma amintattu lafiya lau suke a ko yaushe.

Markus 7:1-13
1. To, da Farisiyawa suka taru a wurinsa tare da waɗansu daga cikin malaman Attaura da suka zo daga Urushalima,
2. suka lura waɗansu almajiransa na cin abinci da hannuwa marasa tsarki, wato marasa wanki.
3. Domin Farisiyawa da dukan Yahudawa ba sa cin abinci sai sun wanke hannu sarai tukuna, saboda bin al'adun shugabanninsu.
4. In sun komo daga kasuwa kuwa, ba sa cin abinci sai sun yi wanka tukuna. Akwai kuma waɗansu al'adu da yawa da suka gada suke kiyayewa, kamar su wankin ƙore, da tuluna, da daruna.
5. Sai Farisiyawa da malaman Attaura suka tambaye shi, “Don me almajiranka ba sa bin al'adun shugabanni, sai su riƙa cin abinci da hannuwa marasa tsarki?”
6. Sai ya ce musu, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku, munafukai! Yadda yake a rubuce cewa, ‘Al'umman nan a baka kawai suke girmama ni, Amma a zuci nesa suke da ni.
7. A banza suke bauta mini, Domin ƙa'idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.’
8. Kuna yar da umarnin Allah, kuna riƙe da al'adun mutane.”
9. Sai ya ce musu, “Lalle kun iya yar da umarnin Allah don ku bi al'adunku!
10. Domin Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ da kuma, ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwa tasa, sai lalle a kashe shi.’
11. Amma ku kukan ce, ‘In mutum ya ce wa ubansa ko uwa tasa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni ya zama Korban,” ’ (wato an sadaukar),
12. shi ke nan fa, ba saura ku bar shi ya yi wa ubansa ko uwa tasa aikin kome.
13. Ta haka kuke banzanta Maganar Allah ta wajen al'adunku na gargajiya. Kun kuwa cika yin irin waɗannan abubuwa.”